Rahotanni sun nuna cewa yarjejeniyar da ake tattaunawa tsakanin Amurka da Iran ta haɗa da shirin kafa wata gidauniyar zuba jari ta dala biliyan 300 domin tallafa wa tattalin arzikin Iran da bunƙasa haɗin gwiwar kasuwanci tsakanin ɓangarorin biyu.
A cewar rahoton Reuters, za a samar da mafi yawan kuɗaɗen ne daga kamfanoni masu zaman kansu daga Amurka, ƙasashen Gulf, Asiya, Afirka da Kudancin Amurka, ba tare da tallafin kai tsaye daga gwamnatoci ba.
An bayyana cewa gidauniyar, wadda za a kira “Gidauniyar Gyara da Ci Gaba”, za ta mayar da hankali kan zuba jari a fannoni kamar makamashi, sufuri, harkokin tashoshin jiragen ruwa da masana’antu.
Rahoton ya kuma ce Iran ta fara neman diyya ta dala biliyan 400 daga Amurka, amma bayan rashin cimma matsaya a kan hakan ne aka samar da wannan tsarin na gidauniyar zuba jari.