Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiDireban adaidaita sahu ya rasa ransa sakamakon rikici tsakaninsu da 'yan sanda...

Direban adaidaita sahu ya rasa ransa sakamakon rikici tsakaninsu da ‘yan sanda a jihar Taraba

Wani direban adaidaita sahu ya rasu a ranar Talata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin jami'an 'yan sanda da masu sana'ar adaidaita sahu a birnin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Wani direban adaidaita sahu ya rasu a ranar Talata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin jami’an ‘yan sanda da masu sana’ar adaidaita sahu a birnin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a yankin Road Block, yayin da jami’an ‘yan sanda ke gudanar da sintiri.

Shaidu sun ce wani ɗan sanda ya fito daga motar sintiri domin kama wani direban adaidaita sahu, lamarin da ya haddasa haɗuwar wasu kekuna biyu masu ɗauke da fasinjoji.

Bayan faruwar hatsarin, masu adaidaita sahu sun taru tare da toshe hanya domin nuna rashin amincewarsu, lamarin da ya haddasa cunkoson ababen hawa.

Mazauna yankin sun ce zanga-zangar ta ƙara tsananta bayan da jami’an ‘yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi zargin cewa wani ɗan sanda ne ya harbe ɗaya daga cikin direbobin adaidaita sahun har ya mutu. Sun kuma ce ana yawan samun saɓani tsakanin masu adaidaita sahu da jami’an ‘yan sanda, musamman kan zargin karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba yayin sintirin dare.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta musanta zargin cewa jami’anta sun buɗe wa masu zanga-zangar wuta.

Kakakin rundunar, ASP Victor Mshelizah, ya ce mamacin na ɗaya daga cikin direbobin adaidaita sahun da suka yi hatsari, ba wai an harbe shi ba.

A cewarsa, jami’an suna gudanar da aikin binciken ababen hawa ne lokacin da wani direban adaidaita sahu ya kauce wa wurin binciken ta hanyar shiga layin da bai dace ba, inda ya yi karo da wani adaidaita sahu.

Ya ƙara da cewa shugaban ofishin ‘yan sanda na yankin ya tabbatar da cewa ba a yi harbi ba, yayin da aka garzaya da mutum biyu da suka samu munanan raunuka a hatsarin zuwa asibiti domin samun kulawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments