Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na samar da babura masu ƙafa uku guda 10,000 da ke aiki da lantarki nan da watan Agustan 2026, domin rage matsalolin sufuri da kuma inganta zirga-zirga a faɗin ƙasar.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sabunta tsarin sufuri da sauƙaƙa jigilar kaya da fasinjoji.
A cewarsa, Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas (NEDC) ce za ta jagoranci rabon waɗannan babura, yayin da aka shirya faɗaɗa shirin zuwa sauran yankunan ƙasar ta hannun hukumomin raya yankuna.
Shettima ya kuma jaddada cewa gwamnati na ci gaba da bunƙasa amfani da iskar gas ta CNG da kuma inganta tashoshin jiragen ruwa da hanyoyin jigilar kaya domin rage tsadar sufuri da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.