Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa gwamnatinsa za ta bai wa Iran Dala miliyan 300, yana mai bayyana rahoton a matsayin ƙage mara tushe.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a dandalinsa na Truth Social, Trump ya ce babu wata yarjejeniya da ta ƙunshi irin wannan biyan kuɗi, yana mai jaddada cewa manufar yarjejeniyar ita ce tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makaman nukiliya.
Mataimakin shugaban ƙasar, JD Vance, ya ce Iran za ta iya amfana da gagarumin ci gaban tattalin arziki idan ta cika dukkan sharuɗɗan da aka gindaya mata.
Sai dai ya bayyana cewa har yanzu akwai wasu batutuwa da ke jiran tattaunawa kafin a fitar da cikakken bayani kan yarjejeniyar.
A nata ɓangaren, Iran ta ce abin da aka samu a tattaunawar ya samo asali ne daga jajircewa da tsayin dakan da ƙasar ta nuna yayin rikicin.