Mutane takwas sun rasa rayukansu bayan wani jirgin yaƙi kirar B-52 Stratofortress na rundunar sojin saman Amurka ya yi hatsari jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin saman Edwards Air Force Base da ke jihar California.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin na kan wani gwajin aiki ne lokacin da ya faɗi da misalin ƙarfe 11:20 na safe, inda hukumomin sojin suka bayyana cewa hatsarin ya kasance mai muni kuma babu wanda ya tsira daga cikinsa.
Daga cikin waɗanda suka mutu akwai jami’an soja, ma’aikatan gwamnati, ‘yan kwangilar gwamnati da kuma ma’aikata biyu na kamfanin Boeing da ke cikin jirgin a lokacin da hatsarin ya faru.
Hukumomin Amurka sun ce an fara gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin, yayin da ake ci gaba da sanar da iyalan mamatan da kuma tattara bayanai kan abin da ya janyo aukuwar lamarin.