Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira biliyan 57.78 kan harkokin tsaro a watanni hudun farko na shekarar 2026, amma duk da haka matsalar rashin tsaro na ci gaba da tsananta a sassa daban-daban na Najeriya.
Wani rahoto ya nuna cewa duk da makudan kudaden da aka ware domin inganta tsaro, hare-haren ‘yan bindiga, sace-sacen mutane da sauran laifuffuka na ci gaba da jefa al’umma cikin fargaba.
Rahoton ya kara da cewa cikin kasa da mako guda, an samu aukuwar laifuffukan da suka shafi tsaro har guda 98 a fadin kasar, yayin da hare-hare da garkuwa da mutane suka kai 51, lamarin da ke nuna yadda kalubalen tsaro ke kara muni.