Rahotanni sun nuna cewa har yanzu Hajiya Amina Abubakar, matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, na ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da mutane duk da rasuwar mijinta.
An sace Manjo Janar Rabe da matarsa ne a ranar 30 ga Mayu, 2026, bayan da wasu ’yan bindiga suka tare motarsu a kan hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli da ke ƙaramar hukumar Matazu a jihar Katsina.
Kafin rasuwarsa, wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna Janar Rabe tare da matarsa suna isar da saƙon masu garkuwar ga gwamnati da al’umma.
A cikin bidiyon, Hajiya Amina ta bayyana cewa masu garkuwar sun nemi a saki wasu mutane uku da suka ambaci sunayensu da Sani, Aminu da Nasiru.
Ta kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da shugabannin wasu ƙananan hukumomi da su taimaka wajen cika bukatun masu garkuwar domin a samu damar sake su.
A ranar Asabar, Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu’azu, ya tabbatar da rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar.
Ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka haɗa da ciwon sukari da hawan jini yayin da yake tsare a hannun masu garkuwar.
Dakta Mu’azu ya bayyana rasuwar tsohon jami’in sojin a matsayin babban rashi ga iyalansa, Jihar Katsina da kuma Najeriya baki ɗaya, yayin da ake ci gaba da fatan ganin an kuɓutar da Hajiya Amina cikin koshin lafiya.