Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSowore ya bukaci ’yan Najeriya su fito zanga-zanga kan rashin tsaro

Sowore ya bukaci ’yan Najeriya su fito zanga-zanga kan rashin tsaro

Fitaccen mai rajin kare hakkin jama’a kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya bukaci ’yan Najeriya su gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da harkokin tsaro.

Sowore ya bayyana hakan ne ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, inda ya yi kira ga jama’a a matakin jihohi, kananan hukumomi da unguwanni da su fito domin nuna adawa da matsalolin da kasar ke fuskanta.

Ya ce rashin tsaro da sauran kalubalen da suka addabi Najeriya na bukatar daukar matakin gaggawa daga gwamnati.

Kiran nasa na zuwa ne yayin da kasar ke ci gaba da fama da hare-haren ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments