Wata gobara da ta tashi a daren Juma’a ta lalata kadarori da dama, daga ciki har da shaguna da ofisoshi, a kan titin Murtala Mohammed Way kusa da bankin FCMB a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.
A cikin wata sanarwa, Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta hannun Kakakina, Saminu Yusuf Abdullahi, ta ce ta samu kiran neman dauki da misalin karfe 10:54 na dare a ranar 11 ga Yunin 2026, inda aka sanar da ita aukuwar gobarar.
Sanarwar ta ce:
“Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano na sanar da al’umma cewa a ranar 11 ga Yunin 2026 da misalin karfe 22:54, Sashen Karbar Kiran Gaggawa ya samu rahoton tashin gobara daga daya daga cikin jami’anmu, HFS Ibrahim Sabo, a kan titin Murtala Mohammed Way kusa da bankin FCMB a karamar hukumar Fagge.”
Hukumar ta bayyana cewa nan take aka tura jami’an kashe gobara daga hedikwatar hukumar da sauran tashoshin kashe gobara na birnin Kano domin shawo kan lamarin.
Bayan isa wurin, jami’an sun tarar da wani gini mai bene daya da kuma wani babban wurin kasuwanci a fili mai fadin kusan kafa 300 da 200 na ci da wuta.
Binciken farko ya nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga kasuwar kayan motoci da aka yi amfani da su, wato Tokumbo Market, inda ta lalata tarin kadarori masu yawa kafin ta bazu zuwa wasu gine-ginen da ke kusa.
Gobarar ta kuma bazu zuwa saman bene na ginin Kanawa Building, inda ta lalata ofisoshi biyu, falo biyu, bandakuna biyu da kuma daki girki guda. Haka kuma ta shafi shaguna biyu da ke kasan ginin mallakar kamfanin TUSRAYS NIG. LTD.
Hukumar ta ce, “Abin da ya haddasa gobarar shi ne tartsatsin wutar lantarki.”
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Sani Anas, ya shawarci jama’a da su dauki duk matakan kariya domin hana aukuwar gobara tare da gaggauta sanar da tashar kashe gobara mafi kusa idan wani lamari makamancin haka ya faru.