Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci gwamnatocin jihohi su daina kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga, tana mai cewa irin wadannan yarjejeniyoyi ba sa samar da zaman lafiya mai ɗorewa, kuma kan iya ƙara ƙarfafa aikata laifuka.
Haka kuma, majalisar ta umarci Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya da Cibiyar Kula da Tsaron Intanet ta Kasa su gano tare da kama ‘yan bindigar da ke amfani da kafafen sada zumunta, musamman TikTok, wajen mu’amala da jama’a tare da nuna tarin kuɗaɗe da ake zargin sun samo daga ayyukan laifi.
Matakin ya biyo bayan kudirin da Sanata Sunday Karimi ya gabatar kan hare-haren da ake ci gaba da kai wa al’ummomi a yankin Kogi ta Yamma