Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiObi: Kada a hukunta Fulani gaba ɗaya saboda laifukan yan ta’addan cikin...

Obi: Kada a hukunta Fulani gaba ɗaya saboda laifukan yan ta’addan cikin su

Peter Obi, ya yi kira ga al’ummar Najeriya da su guji ɗora laifin wasu mutane kan daukacin kabilar Fulani, yana mai cewa hakan na ƙara rura wutar ƙiyayya da rarrabuwar kawuna a ƙasa.

A wata sanarwa da ya fitar, Obi ya bayyana cewa ya kamata a rika kallon masu aikata laifi a matsayin mutane ɗaiɗaiku, ba tare da jingina ayyukansu ga wata ƙabila ko al’umma baki ɗaya ba.

Ya ce shi ma a matsayinsa na ɗan kabilar Igbo ya taɓa fuskantar wariya da zarge-zarge saboda asalinsa, lamarin da ya nuna cewa matsalar nuna bambanci ta shafi kabilu daban-daban a Najeriya.

Obi ya nuna damuwa kan yadda ake kallon Fulani gaba ɗaya a matsayin masu laifi saboda laifukan wasu tsirarun mutane, yana mai jaddada cewa ta’addanci, sata da garkuwa da mutane laifuffuka ne da ba su da alaƙa da wata ƙabila.

Ya buƙaci jami’an tsaro da hukumomin da abin ya shafa su mayar da hankali wajen gano masu laifi tare da hukunta su bisa doka, maimakon zargin wata al’umma baki ɗaya.

Haka kuma ya bukaci ‘yan Najeriya su rungumi zaman lafiya da haɗin kai tare da kaucewa ra’ayoyin wariya da wasu ke amfani da su wajen cimma manufofinsu na siyasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments