Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKu ci gaba da addu’a kan matsalar tsaro – Akpabio ya yi...

Ku ci gaba da addu’a kan matsalar tsaro – Akpabio ya yi kira ga yan Najeriya

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da nuna haƙuri tare da dagewa da addu’o’i domin ganin an kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ke fuskantar ƙasar.

Akpabio ya bayyana cewa haɗin kai, goyon bayan jama’a da kuma addu’a na daga cikin muhimman abubuwan da za su taimaka wajen cimma zaman lafiya mai ɗorewa.

Ya nuna kwarin gwiwa cewa da ƙoƙarin jami’an tsaro da haɗin kan al’umma, za a samu nasarar magance matsalolin tsaro tare da tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar.

Haka kuma ya buƙaci ’yan Najeriya su ci gaba da ba hukumomin tsaro goyon baya da bayanan da za su taimaka wajen yaƙi da miyagun laifuka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments