Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKwastam sun kama jami’in 'yan sandan Nijar dauke da bindiga a iyakar...

Kwastam sun kama jami’in ‘yan sandan Nijar dauke da bindiga a iyakar Katsina

Jami’an Hukumar Kwastam ta Najeriya sun kama wani jami’in rundunar ’yan sandan Jamhuriyar Nijar a mashigar iyakar Jibiya da Magama da ke jihar Katsina bayan ya nuna rashin haɗin kai yayin binciken tsaro.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Juma’a, 5 ga watan Yuni, 2026, yayin da jami’an kwastam ke gudanar da bincike na yau da kullum a kan matafiya da masu shiga da fita ta iyakar.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa jami’an sun dakatar da mutumin ne domin tabbatar da ko wanene shi da kuma inda ya dosa, amma ya nuna turjiya tare da tayar da hayaniya.

Sakamakon haka, jami’an suka tsare shi domin gudanar da ƙarin bincike.

A yayin binciken da aka yi masa, an gano bindiga kirar pistol tare da harsasai guda biyar masu girman milimita tara a hannunsa.

Daga bisani, bincike ya tabbatar da cewa mutumin jami’i ne na rundunar ’yan sandan ƙasar Nijar da ya shigo Najeriya ta hanyar mashigar iyakar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments