Hukumar kula da ’yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta bayyana cewa matsalolin rashin tsaro da rikice-rikicen da ke addabar wasu sassan Najeriya sun tilastawa karin mutane 8,521 tsallakawa zuwa kasashen Nijar, Chadi da Kamaru domin neman mafaka tsakanin watan Disamban 2025 zuwa Mayun 2026.
Wani sabon bincike da aka gudanar tare da hadin gwiwar kungiyoyin kasa da kasa masu kula da ’yan gudun hijira da kuma hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ya nuna cewa adadin ’yan Najeriya da suka yi rajista a matsayin ’yan gudun hijira a wadannan kasashe ya kai mutum 416,184.
Rahoton ya nuna cewa Jamhuriyar Nijar ce ke dauke da mafi yawan ’yan gudun hijirar Najeriya, inda adadinsu ya kai 268,967.
Wannan adadi ya karu da mutane 10,608 cikin watanni shida kacal.
Har ila yau, alkaluman sun nuna cewa jihar Sokoto na daga cikin wuraren da aka fi samun masu barin gidajensu saboda matsalar tsaro.
Adadin mutanen da suka tsallaka daga jihar ya tashi daga 88,562 zuwa 181,526 a cikin wannan lokaci.
A bangaren Kamaru kuwa, akwai ’yan gudun hijirar Najeriya 125,192, inda mafi yawansu ke zaune a sansanin Minawao.
Ita ma Jamhuriyar Chadi na karbar ’yan Najeriya 22,025 da suka tsere daga tashe-tashen hankula da hare-haren masu dauke da makamai.
UNHCR ta ce wadannan alkaluma na nuna yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da tilastawa dubban ’yan Najeriya barin gidajensu da kuma neman kariya a kasashen makwabta.