Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHadimin El-Rufa’i ya zargi ICPC da hana tsohon gwamnan samun kulawar likita

Hadimin El-Rufa’i ya zargi ICPC da hana tsohon gwamnan samun kulawar likita

Hadimin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya zargi Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) da rashin ba shi kulawar lafiya duk da korafe-korafen da ya yi kan matsalar idanunsa.

A cewar Muyiwa Adekeye, wanda ya taba zama mai taimaka wa El-Rufa’i kan harkokin yada labarai, tsohon gwamnan na fama da kumburi, jajayen ido da kuma kaikayi yayin da yake ci gaba da kasancewa a tsare.

Adekeye ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa inda ya ce duk da tsanantar matsalar, ba a kai El-Rufa’i wurin likita domin a duba lafiyarsa ba.

An tsare El-Rufa’i ne dai bayan dawowarsa daga kasar Masar bisa wasu zarge-zarge da ake bincike a kansu.

Tun daga lokacin yake hannun hukuma, inda ya gudanar da bukukuwan azumi da Sallar Layya a tsare.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ICPC ba ta fitar da wata sanarwa kan zarge-zargen da ake yi mata na kin samar masa da kulawar lafiya ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments