Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiBa na bukatar duk wani tallafi daga Amurka – Netanyahu

Ba na bukatar duk wani tallafi daga Amurka – Netanyahu

Netanyahu ya ce Isra’ila ta yaba da taimakon Amurka, amma ta riga ta fara dogaro da karfinta.

Netanyahu ya ce Isra’ila na godiya ga Amurka kan tallafin da ta bayar na tsawon shekaru, amma yanzu ba ta bukatarsa.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da wakiliyar tashar talabijin ta CNBC a ofishinsa.

Jawabin nasa ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara da tattaunawa kan alakar da ke tsakanin Amurka da Isra’ila, musamman yadda Washington ke bai wa Tel Aviv goyon baya a fannoni daban-daban.

Netanyahu ya yi kalaman ne yayin wani batun haɗin gwiwa da tallafin da Amurka ke bai wa Isra’ila ke ci gaba da jan hankalin masu ruwa da tsaki a duniya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments