Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaINEC ta yi martani kan jita-jitar yaduwar bayanan masu zabe

INEC ta yi martani kan jita-jitar yaduwar bayanan masu zabe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC ta yi karin bayani kan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan yaduwar wasu bayanan rajistar masu kada kuri’a da suka shafi wani dan siyasa a kafafen sada zumunta.

Takaddamar ta samo asali ne bayan mai magana da yawun Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, Lere Olayinka, ya wallafa wasu bayanai da suka danganci fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Emeka Ike.

Rahotanni sun nuna cewa Emeka Ike ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar AMAC/Bwari a Abuja karkashin jam’iyyar NDC.

Bayan wannan sanarwa, Olayinka ya yi tsokaci kan sauya wurin rajistar zaben jarumin daga jihar Imo zuwa Abuja, inda ya wallafa wasu hotuna da ke dauke da bayanan rajistarsa na zabe.

Matakin ya haifar da cece-kuce a tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka nuna damuwa tare da tambayar yadda aka samu damar fitar da bayanan da ake ganin na sirri ne daga kundin bayanan INEC.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments