Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta sanar da cafke wata mata da ake zargi da hannu a kisan uwargidan mijinta a unguwar Gwargwaje da ke cikin birnin Zariya.
Rahotanni sun nuna cewa matar da ake zargin ta kai wa uwargidan mijinta hari da wuƙa, lamarin da ya yi sanadin rasuwarta.
’Yan sanda sun ce sun kama wadda ake zargin tare da fara gudanar da bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin da kuma tabbatar da gaskiyar zarge-zargen da ake yi mata.