Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya musanta rade-radin da ke cewa yana shirin ajiye mukaminsa, yana mai tabbatar da cewa zai ci gaba da jagorantar ƙasar muddin yana raye.
A cikin wani bidiyo da kafar yada labarai ta Tasnim News Agency ta wallafa, shugaban ya bayyana cewa ba shi da niyyar yin murabus duk da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta.
Pezeshkian ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen fuskantar kalubalen da ke gabanta, yana mai cewa ko dai za su yi nasara a kan manufofinsu ko kuma su sadaukar da rayukansu a wannan tafiya.
Jawabin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yada jita-jitar cewa yana tunanin sauka daga kan mulki.