Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasa'Yan Najeriya na cikin wani hali - PDP ta zargi gwamnatin Tinubu...

‘Yan Najeriya na cikin wani hali – PDP ta zargi gwamnatin Tinubu da gaza wa

Jam’iyyar PDP ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gaza kare ’yan Najeriya a gida, a kasuwa, a wuraren aiki da kuma kan tituna.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Kabiru Turaki, ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Talata.

Taron ya gudana ne a gidan gwamnatin Bauchi da ke Asokoro, inda sabon Kwamitin zartarwar jam’iyyar na kasa PDP ke gudanar da zama tun bayan rufe hedikwatar jam’iyyar da rundunar ’yan sanda ta yi a watan Nuwamba.Turaki ya caccaki matsayin tsaro a ƙasar, yana mai cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta sake duba dabarun tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce: “Mun yarda cewa halin da ake ciki yanzu ya nuna ba a cikin kariya ’yan ƙasa suke ba. Ba su cikin tsaro a tituna, a wuraren aikinsu — ko ofisoshi ne, ko gona, ko kasuwanni. Haka nan babu tsaro a gidajensu. Ya zama dole a kawo ƙarshen wannan yanayi na rayuwa cikin tsantsar tsoro.”

Shugaban ya kuma soki gwamnatin tarayya saboda gazawar da ya ce ta nuna wajen cika muhimman abubuwan da al’umma ke tsammani daga gwamnati.

Ya ce: “Yawaitar sace-sace da kashe-kashe da ake fama da su ya nuna gwamnatin APC ba ta kai matsayin da ’yan Najeriya ke tsammani ba. Muna kira ga gwamnati ta tashi tsaye kuma ta yi nazari kan tsarin tsaron ƙasa.”

Turaki ya ƙara cewa ba daidai ba ne a kira gwamnoni shugabannin jami’an tsaro amma ba su da ikon umartar hukumomin tsaro da ke jihohinsu.Game da shirye-shiryen zaɓen gwamnan Jihar Osun, ya ce kwamitin PDP na ƙasa ya gamsu da tsarin zaben fitar da gwanin da ake gudanarwa.

Ya bayyana cewa an amince da sakamakon zaɓen wakilan da aka gudanar a jihar, tare da yabawa yadda ake tafiyar da harkokin jam’iyyar ba tare da hatsaniya ba.

A kan batun shari’o’in da suka shafi jam’iyyar, Turaki ya ce lauyoyin PDP sun tabbatar musu cewa suna da gamsassun hujjoji musamman kan rufe ofisoshin jam’iyyar da aka yi, inda ya ce nan ba da jimawa ba doka za ta yi aikinta.

Ya tabbatar da cewa sabon kwamitin PDP na nazarin bayanan mika mulki daga shugabannin da suka gabata domin tabbatar da ci gaba ba tare da tangarɗa ba.

Game da batun Ministan Abuja, Nyesom Wike, da tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, da sauran mutum tara da aka kora a taron PDP da aka yi a Ibadan, Turaki ya ce rahotanni sun isa gare su, kuma an aika musu da takardun korar su ta hanyar ofishin aika saƙonni.

Ya shawarci INEC, rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su lura cewa waɗannan mutanen ba su cikin jam’iyyar PDP.

A kan matsayin Gwamna Ademola Adeleke, Turaki ya ce kowane ɗan ƙasa na da ’yancin sauya jam’iyyar da ya ga dama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments