Rahotanni sun bayyana cewa ana ƙazamin fada a yankin kudancin Sudan tsakanin rundunar sojin kasar da kuma kungiyar RSF.
Sojojin sun ce sun ƙwace garin Mabsouta da ke kudancin Kordofan, kuma dakarun rundunar da ke Arewacin Kordofan na fama da harin jiragen sama marassa matuka.
Mazauna babban birnin – El-Obeid, sun ce sun ga hayaki na tashi daga wani sansanin soji da ke birnin.
Duk wani yunƙuri na dakatar da bude wuta ya ce tura inda bangarorin biyu ke kafewa kan wasu sharudda da ba za su yiwu ba.