Wannan amincewar wani muhimmin mataki ne da aka ɗauka domin magance matsalar ƙarancin ruwa da ta daɗe tana addabar al’ummar jihar, kamar yadda Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta jihar ta bayyana a cikin wata sanarwa bayan zaman Majalisar Zartarwa ta jihar.
Sanarwar, wadda mukaddashin kwamishinan ma’aikatar, Dakta Dahir Muhammad Hashim ya sanya wa hannu, ta ce wannan shiri ya shafi muhimman wuraren samar da ruwa da suka rage ƙarfin aiki, lamarin da ya janyo ƙarancin ruwa a jihar.
Aikin ya haɗa da gyaran cibiyar tace ruwa ta Tamburawa tare da dawo da tashar famfon ruwana farko a kan kuɗi Naira biliyan 9.9.
Haka kuma za a gyara tashar famfon ruwa da cibiyar tace ruwa ta Challawa, tare da dawo da rijiyoyin ajiyar ruwa na Goron Dutse, a kan kuɗi naira biliyan 11.39.
Dakta Hashim ya bayyana cewa wannan ɗaya ne daga cikin manyan zuba jari a bangaren ruwa a cikin ‘yan shekarun nan, yana mai cewa lallai akwai buƙatar wannan mataki cikin gaggawa.
Ya ƙara bayyana cewa cibiyar Tamburawa wadda aka gina domin samar da lita miliyan 150 na ruwa a rana, a halin yanzu tana aiki ne da kusan kashi 27 cikin ɗari kacal, sakamakon lalacewar da ambaliyar ruwa ta janyo tun shekarar 2022, musamman a tashar famfon ruwa.
Haka nan cibiyar Challawa, wadda ke da ƙarfin samar da lita miliyan 220 a rana, ita ma tana aiki da ƙasa da kashi 30 cikin ɗari.
A hade, wadannan cibiyoyi an gina su ne domin samar da lita miliyan 370 na ruwa a rana, amma yanzu suna samar da ƙasa da haka sosai, wanda hakan ke jawo ƙarancin ruwa a fadin jihar.
Bugu da ƙari, rijiyoyin ajiyar ruwa na Goron Dutse, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen rarraba ruwa a cikin birnin Kano, sun daina aiki gaba ɗaya sakamakon lalata wasu muhimman kayan aikinsu.
Dakta Hashim ya ce waɗannan matsaloli suna nuna girman ƙalubalen da ake fuskanta, amma kuma suna nuna inda gwamnati ta maida hankali wajen magance su kai tsaye.
Ya tabbatar wa al’umma cewa wannan shirin zai dawo da ƙarfin samar da ruwa, inganta yadda ake rarraba shi, tare da tabbatar da samun ruwa yadda ya kamata a jihar.
Duk da cewa ya amince da irin wahala da jama’a ke fuskanta sakamakon ƙarancin ruwa, ya jaddada cewa gwamna na da ƙudirin magance wannan matsala ta hanyar da za ta ɗore, kuma ana sa ran cewa nan ba da daɗewa ba matsalar ƙarancin ruwa a Kano za ta ragu sosai ko ma ta ƙare gaba ɗaya.
Ya kuma buƙaci haɗin kan jama’a, musamman wajen kare kayayyakin samar da ruwa daga ɓarna, domin hakan na daga cikin abubuwan da ke janyo matsalolin katsewar ruwa akai-akai.
Gwamnatin jihar Kano ta sake jaddada aniyarta na samar da ingantaccen ruwa da kuma inganta rayuwar al’umma ta hanyar ci gaba da saka jari a muhimman ababen more rayuwa.