Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano AKTH ta bullo da tsarin bayar da katin shaida, I.D Card ga ‘yan uwa ko masu kula da marasa lafiya da ke kwance a asibiti.
Babban Daraktan Lafiya na asibitin, Farfesa Abdurrahman Abba-Sheshe, ya bayyana wannan sabon tsari, yana mai cewa an kirkiro shi ne domin tabbatar da tantance sahihin ‘yan uwan marasa lafiya tare da inganta tsaro, kulawa da sa ido a cikin asibitin.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’ar yada labarai ta asibitin, Maryam Aminu-Usman, ta fitar a ranar Laraba.
Ya ce kowane mara lafiya da aka kwantar zai samu mai kula da shi guda daya kacal wanda za a ba katin shaidar. Idan aka sauya mai kula, dole ne a mika katin ga wanda zai karbi aikin kula.
Haka kuma, hukumar asibitin ta bukaci jama’a da su guji zuwa ziyara da yawa ko tare da kananan yara, domin suna da saukin kamuwa da cututtuka masu yaduwa.
Babban Daraktan ya bayyana cewa cunkoso da taruwar jama’a a dakunan jinya lokacin ziyara na hana marasa lafiya samun hutawa yadda ya kamata, sannan yana kawo cikas ga matakan kariya daga cututtuka.
Hukumar ta kuma bukaci jama’a da su kiyaye lokacin ziyara kamar yadda aka tsara bisa kwanakin mako, karshen mako da kuma ranakun hutu na gwamnati.