Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiShugabannin ƙananan hukumomi 16 na Kano ta Kudu sun goyi bayan Alhassan...

Shugabannin ƙananan hukumomi 16 na Kano ta Kudu sun goyi bayan Alhassan Rurum ya tsaya takarar sanata

Shugabannin ƙananan hukumomi guda 16 daga Kano ta Kudu sun bayyana goyon bayansu ga Kabiru Alhassan Rurum a matsayin ɗan takarar da suke so ya tsaya takarar kujerar Sanata a karkashin jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Shugabannin ƙananan hukumomi guda 16 daga Kano ta Kudu sun bayyana goyon bayansu ga Kabiru Alhassan Rurum a matsayin ɗan takarar da suke so ya tsaya takarar kujerar Sanata a karkashin jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

A wata sanarwa da suka fitar bayan sun tattauna da majalisunsu, shugabannin jam’iyya da ‘yan majalisa a yankin a ƙarshen makon nan, shugabannin sun ce sun yanke wannan hukunci ne domin mara wa Rurum baya, wanda a halin yanzu yake wakiltar mazabar Rano/Kibiya/Bunkure a Majalisar Wakilai, domin ya fafata da Sanatan da ke kan kujerar yanzu, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila.

Sanarwar ta nuna cewa an cimma wannan matsaya ne gaba ɗaya ba tare da sabani ba, tare da jaddada muhimmancin ci gaba da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin ‘yan jam’iyya.

Sun kuma ƙara da cewa wannan goyon baya na da nufin ƙarfafa haɗin kai da tabbatar da kyakkyawan wakilci ga al’ummar Kano ta Kudu a matakin ƙasa.

Da yake tabbatar da wannan lamari, mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Bebeji, Ali Sarkin Yaki, ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin ceto jam’iyyar a zaɓen da ke tafe.

Ya bayyana cewa hakan ya zama dole domin hana jam’iyyar rasa kujerar Sanata a hannun ‘yan adawa a zaɓen 2027.

Da aka tuntubi wani na kusa da Sanatan, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sun san da wannan matsaya amma sun ƙi yin tsokaci a halin yanzu.

“Mun gani, amma ba lokacin yin magana bane tukuna. Za mu yi magana kan duk abubuwan da aka taso da su nan gaba,” in ji shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments