Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ƙungiyoyin sa-kai ne sun kashe mutane uku da suka je zaman makoki, sannan suka sace wasu biyu a daren Asabar, yayin da suke dawowa daga jana’iza a yankin Sati Ikov, karamar hukumar Ushongo a Jihar Benue.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da mutanen ke dawowa daga jana’izar, inda suka ci karo da ‘yan bindigar.
Dan majalisar dokokin jihar da ke wakiltar yankin Ushongo, Simon Gabo, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai nuna damuwa kan yadda hare-haren ke ƙaruwa a yankin.
Ya ce a cikin makonni biyu da suka gabata, an yi ta samun irin wadannan hare-hare, wanda ya jawo asarar rayuka da dama.
Mutanen da aka kashe sun hada da Bem Msughter, Aondo Chia da Sunday Terwase.
Haka kuma, an sace Aondongu Amos-Mbanyion, wanda ke sana’ar POS, da kuma Misis Arinze, ‘yar kasuwa mai sayar da magungunan gargajiya.
Gabo ya kara da cewa maharan kan ratsa kogi daga karamar hukumar Katsina-Ala zuwa Ushongo domin kai hare-hare, sannan su koma.
Ya ce yankin na da dazuzzuka da tsaunuka, wanda ke sauƙaƙa wa ‘yan bindigar boyewa.
Ya tabbatar da cewa ya sanar da jami’an tsaro, kuma tuni jami’an ‘yan sanda suka isa yankin domin fara bincike.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar bai samu damar yin karin bayani ba a lokacin da aka tuntube shi.