Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da yiwa ma’aikatanta ƙarin alawus-alawus na tafiye-tafiye, da kuma alawus ɗin kama guraren kwana idan buƙatar hakan ta taso a dalilin aiki.
Haka kuma hukumar ta ce wannan ƙarin wanda ya ninka da kaso 100 zai shafi dukannin ma’aikacin gwamnatin da aiki ya kama shi a wajen Ofis, ba tare da la’akari da ko ina bane.
Baya ga hakan hukumar ta bijiro da wani tsarin baiwa ma’aikata masu ritaya wani ƙunshin kuɗin sallama idan lokacin ajiye aiki yayi, wanda za’a yi shi ƙarƙashin hukumar kula da ƴan Fansho.
Da take sanar da wannan ci gaba, shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya Didi Walson-Jack, ta ce sabon tsarin ya tanadi baiwa ma’aikatan da zasu yi ritaya kaso 100 na kuɗaɗen albashinsu na shekara, da nufin nuna godiya ga sadaukarwarsu ga ƙasa.
A cewar ta dukannin ma’aikatan gwamnatin tarayya za su amfani wannan sabon tsari ba tare da la’akari da tsarin biyan albashin ma’aikaci ba.