Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeBa tattaunawa da Amurka ne ya kai mu Pakistan ba – Iran

Ba tattaunawa da Amurka ne ya kai mu Pakistan ba – Iran

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya isa birnin Islamabad na Pakistan a wani ɓangare na ci gaba da shirye-shiryen faɗaɗa tattaunawar zaman lafiya da kuma samar da mafita da zata kawo ƙarshen yaƙin da ƙasar ke yi tsakaninta da Isra’ila da Amurka.

Wannan ziyara dai ta bada hasken cewa akwai yiwuwar a cimma jituwa a yaƙin da aka kwashe makonni 8 ana gabzawa, da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da kuma girgiza tattalin arzikin duniya.

Da yake jawabi shugaban Amurka Donald Trump ya ce wannan ci gaba ne da ke nuna alamun Iran zata amince da jerin dokokin da Amurka ta shimfiɗa mata, duk da dai ya ce bashi da tabbaci game da hakan.

Sai dai kuma a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ce wakilan ƙasar da suka isa Islamabad ba su da shirin ganawa da wakilan Amurka illa, iyaka nazartar halin da ake ciki da kuma tattaunawa da wakilan Pakistan mai shiga tsakani.

Wannan kalamai na zuwa ne a dai-dai lokacin da wakilan Amurka suma suka sauka a birnin na Islamabad, dalilin da ya sanya ake raɗe-raɗin ko ana shirin komawa kan teburin tattaunawa ne.

Babu shakka wannan yaƙi ya girgiza dukannin ƙasashen biyu, a fannin ƙarfin soja da kuma tattalin arziki, yayin da kowanne ɓangare ke shan suka daga sauran ƙasashen duniya game da kawo ƙarshen yaƙin.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments