Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaECOWAS ta bukaci a koma mulkin farar hula a Guinea-Bissau

ECOWAS ta bukaci a koma mulkin farar hula a Guinea-Bissau

Gwamnatin wucin gadi ta Guinea Bissau ta bayyana cewa an yi juyin mulki ne saboda kare martabar dimokuradiyya

Wata babbar tawagar ECOWAS ta nemi shugabannin juyin mulki a Guinea-Bissau da su gaggauta mayar da kasar kan tsarin mulkin dimokuradiyya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Shugaban Sierra Leone, Julius Maada Bio, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ECOWAS, ya yi Allah wadai da kifar da tsohon Shugaba Guniea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo.

Shugaba Bio ya ce:

Sai dai Shugaba na wucin gadi na kasar Guniea Bissau da aka yi juyin mulki, Janar Horta N’Tam, ya ce sun yi juyin mulkin ne don hana ‘yan ta’adda lalata tsarin dimokuradiyya.

An dakatar da Guinea-Bissau daga harkokin ECOWAS da AU, yayin da sojoji suka kafa gwamnati mai membobi 28 ta riƙon ƙwarya don tafiyar da ƙasar.

“Mun sake tabbatar da jajircewarmu wajen dawo da tsarin mulkin doka.”

Za a yanke hukuncin makomar ƙasar a taron shugabannin ƙasashen ECOWAS a ranar 14 ga Disamba.

SourceBBC Hausa
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments