Wata babbar tawagar ECOWAS ta nemi shugabannin juyin mulki a Guinea-Bissau da su gaggauta mayar da kasar kan tsarin mulkin dimokuradiyya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Shugaban Sierra Leone, Julius Maada Bio, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ECOWAS, ya yi Allah wadai da kifar da tsohon Shugaba Guniea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo.
Shugaba Bio ya ce:
Sai dai Shugaba na wucin gadi na kasar Guniea Bissau da aka yi juyin mulki, Janar Horta N’Tam, ya ce sun yi juyin mulkin ne don hana ‘yan ta’adda lalata tsarin dimokuradiyya.
An dakatar da Guinea-Bissau daga harkokin ECOWAS da AU, yayin da sojoji suka kafa gwamnati mai membobi 28 ta riƙon ƙwarya don tafiyar da ƙasar.
“Mun sake tabbatar da jajircewarmu wajen dawo da tsarin mulkin doka.”
Za a yanke hukuncin makomar ƙasar a taron shugabannin ƙasashen ECOWAS a ranar 14 ga Disamba.