Rahotanni sun nuna cewa farashin danyen mai irin su Brent da kuma West Texas Intermediate sun fadi da sama da kashi 10 cikin 100, lamarin da ya kai su mafi karancin matsayi cikin ‘yan makonni.
bayan sanarwar da Iran ta yi na bude mashigar ruwa ta Strait of Hormuz ga zirga-zirgar jiragen ruwa na kasuwanci.
Wannan mataki ya kawo saukin tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda a baya ya haddasa tsadar mai saboda takaita hanyoyin safarar man fetur. 
Mashigar ta Hormuz na daya daga cikin hanyoyin da suka fi muhimmanci a duniya wajen jigilar mai, domin kusan kashi daya cikin hudu na man da ake safararsa ta teku yana bi ta wannan hanya. 
Bude mashigar ya zo ne a daidai lokacin da ake samun yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma kokarin sasanta rikice-rikicen yankin, wanda hakan ya rage fargabar karancin mai a kasuwanni.