Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaAna yunkurin hana majalisa tantance Sulen Garo a matsayin mataimakin Gwamnan Kano

Ana yunkurin hana majalisa tantance Sulen Garo a matsayin mataimakin Gwamnan Kano

Batun maye gurbin mataimakin gwamnan Kano ya haifar da sabon rikici a bangaren shari’a.

Wani sabon rikicin shari’a ya kunno kai dangane da batun maye gurbin mataimakin gwamnan Kano State, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Wasu lauyoyi sun rubuta wasika inda suka bukaci Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da duk wani yunkuri na tantance Murtala Sule Garo har sai an kammala shari’ar da ke gaban kotu.

Daily Nigerian ta wallafa cewa wannan bukata na kunshe ne cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 15 ga Afrilu, 2026, da lauyoyi Suleiman Mohammed & Co. suka aikewa da kakakin majalisar, Jibrin Falgore.

Rahoton ya ce lauyoyin suna wakiltar Kuliyya Muhammad Salihu da wasu mutum biyu da suka shigar da kara kan lamarin tantance Garo a matsayin mataimakin gwamnan Kano.

A cewar lauyoyin, sun riga sun kai ƙara gaban babbar kotun jihar Kano, inda suka kalubalanci yunkurin tantance Garo a matsayin mataimakin gwamna.

Sun bayyana cewa tunda shari’ar tana gaban kotu mai iko, to lamarin ya zama “sub judice”, wato bai dace a ci gaba da daukar wani mataki ba har sai an yanke hukunci.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments