Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta fara bincike kan wasu rahotanni da ke cewa an samu mace-macen fararen-hula da yawa yayin hare-haren sama da ta kai kasuwar Jilli kusa da ƙauyen Fuchimiram a ƙaramar hukumar Geidam ta jihar Yobe, a Arewa maso gabashin ƙasar.
Ranar Lahadi ne dai rundunar sojin ƙasar ta fitar da sanarwar kai hari Jilli inda ta wallafa hotona na harin da suka nuna ababen da ta kira motocin ‘yanta’adda da ma sauran kayan yaƙi da ta kai wa hari a kasuwar.
Sai dai kuma yayin da rundunar sojin saman ta Najeriya ta ce ta yi nasarar kai hari kan wurin da ta kira cibiyar kasuwancin ‘yanta’addaa a Arewa maso gabashin ƙasar, wasu rahotanni na cewa kimanin fararen-hula 200 aka kashe a harin.
A sanarwar da ya fitar, daraktan watsa labaran rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce rundunar “tana ɗaukar duk rahotannin yiwuwar jikkata fararen-hula a matsayin abin damuwa sosai da kuma abin tausayi”.
“Bisa ga wannan jajircewar, babban hafsan sojin sama ya ba da umarnin tura wata tawaga domin yin bincike kan wannan zargi,” in ji sanarwar.
A wata sanarwa da ta fitar tun da farko, rundunar sojin saman Najeriya ta tabbatar da kai hare-haren sama a yankin Jilli amma ba ta bayyana ko an samu mutuwar fararen-hula ba.
An kai hare-haren ne “yayin da muke zafafa ƙoƙarin nemo da kassara ‘yanta’addan da suka kai hari kwanan baya kan dakarun tsaro a fagen yaƙin, kuma an ƙaddamar da hare-haren ne kan ‘yanta’adda masu tserewa domin ƙara haɗuwa a wani wurii,” in ji rundunar sojin saman Najeriya.