Kakakin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya mayar da martani ga kalaman ministan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa ba batun wanda zai kayar da wani a zaɓen 2027 ne ke damun ’yan Najeriya ba, sai dai halin ƙunci da suke ciki.
Ya ce a halin yanzu, abubuwan da suka fi addabar al’umma sun haɗa da rashin tsaro, yunwa da kuma tsadar rayuwa, waɗanda ya bayyana a matsayin manyan ƙalubalen da ke bukatar kulawa ta gaggawa daga gwamnati.
A cewarsa, mayar da hankali kan siyasar gaba, musamman maganar zaɓen 2027, na nuni da rashin fahimtar halin da jama’a ke ciki.
Kakakin ya ƙara da cewa ‘yan Najeriya na fama da matsin rayuwa mai tsanani, inda farashin kayayyaki ke ci gaba da tashi, yayin da rashin tsaro ke hana mutane gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.
Ya jaddada cewa wajibi ne gwamnati ta karkata akalarta wajen magance waɗannan matsaloli domin sauƙaƙa rayuwar al’umma.
Haka kuma, ya yi kira ga shugabanni da masu ruwa da tsaki da su daina jefa jama’a cikin cece-kuce na siyasa, su mayar da hankali wajen samar da mafita ga matsalolin da suka dabaibaye ƙasar.
Ya ce abin da ya kamata ya fi daukar hankali a yanzu shi ne yadda za a inganta tsaro da rage radadin rayuwa, ba wai fafatawar siyasa ba.