Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Katsina ta fara shirye-shiryen auren gata ga matasa 1000 a jihar

Gwamnatin Katsina ta fara shirye-shiryen auren gata ga matasa 1000 a jihar

Dubunnan matasa a Katsina na shirin shiga auren gata da gwamnatin jihar ke daukar nauyi.

Gwamnatin jihar Katsina ta kammala dukkan shirye-shirye na gudanar da rukunin farko na auren gata ga matasa 1000 a Jihar

Gwamnatin ta shirya auren gatan ne ga masu shirin zama ma’aurata 1,000 da aka zaɓo daga ƙananan hukumomi 34 na jihar.

Gwamnatin tare da haɗin gwiwar wata ƙungiyar sa-kai (NGO), Al-Usra Marital Support Foundation, sun shirya taron ƙarawa juna sani da horo na musamman ga masu shirin ma’aurata 1,000 da za su yi auren.

Shugabar ƙungiyar, Dr. Murjanatu Ibrahim-Duwan, ta bayyana cewa horon wanda aka gudanar a ranar Alhamis, 9 ga watan Afirilun 2026, na nufin ƙarfafa martabar iyali da kuma rage yawan mace-macen aure (saki) a cikin al’umma.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments