Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne masu amfani da babura sun yanke hannun wani malami mai suna Isah Sallama yayin wani mummunan hari a karamar hukumar Bunkure ta Jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da daren Laraba a kan hanyar Funkuyi da ke gundumar Buran.
A cewar wata sanarwa daga Sakataren wayar da kai na masarautar Rano, Nasiru Habu Faragai, an kai wa malamin hari ne yayin da yake kokarin taimakawa wani mutum, Malam Sauwanu Hadi, wanda ‘yan fashin ke kokarin kwace masa babur da wayarsa.
Sanarwar ta bayyana cewa da farko maharan sun yi yunkurin harbe Sallama, amma bindigarsu ta kasa aiki.
Bayan hakan, sai suka yi amfani da adda suka yanke masa hannu, inda suka bar shi cikin mummunan hali.
Daga baya, hakimin Bunkure, Alhaji Aminu Isa Umaru, ya kai rahoton lamarin ga Sarkin Rano, Muhammad Isa Umaru.
Da yake mayar da martani, Sarkin ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya umarci a kai rahoton ga jami’an tsaro domin gudanar da cikakken bincike.
Haka kuma, Sarkin ya amince da bayar da gudummawar Naira dubu 100 domin tallafawa jinyar wanda aka ji rauni.
Ya kuma bukaci shugabannin al’umma da jami’an tsaro da su kara kokari wajen dakile ayyukan fashi da sauran laifuka a yankin.