Hukumomin rarraba wutar lantarki ta kasa ta sanar da cewa gwamnatin tarayya za ta yi wani muhimmin gyara game da wutar lantarki.
Rahotanni sun nuna cewa gyaran zai shafi yadda ake rarraba wutar lantarki a jihohin Arewa bakwai, musamman daga safiya zuwa rana.
Hakan yasa kamfanin rarraba wuta na JED ya sanar da al’umma da ke wasu jihohin Arewa da za su samu sauyi a kan yadda suke samun lantarki a wani sako da ya wallafa a a Facebook.
Jihohin da abin zai shafa sun hada da Plateau, Gombe, Bauchi, Borno, Adamawa, Taraba da Yobe galibinsu a Arewa masu Gabashin Najeriya.