Amurka ta umarci jami’anta na diflomasiyya su fice daga Abuja, babban birnin Najeriya, yayin da tsaro ke ”ƙara taɓarɓarewa” a ƙasar.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce ta umarci ma’aikatan gwamnatin Amurka a ofishin waɗanda aikinsu bai zama wajibi ba, da kuma iyalansu su bar ƙasar.
Haka kuma gwamnatin Amurkar ta shawarci ƴan ƙasarta da ke so ko kuma suke shirin zuwa Najeriya da su sake shawara, saboda matsalar tsaro wadda ta haɗa da satar mutane da ayyukan ƙungiyoyin ƴan bindiga.
A jiya Laraba ne hukumomin Najeriyar suka fara shari’ar sama da mutum 500 da ake zargin su da hannu a hare-haren ƴan bindiga, da suka yi sanadiyyar mutuwar dubban jama’a musamman a arewacin ƙasar.