Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiYan bindiga a Zamfara sun kakaba kauyuka harajin Naira miliyan 16 tare...

Yan bindiga a Zamfara sun kakaba kauyuka harajin Naira miliyan 16 tare da ba su wa’adi

A wani sabon hari, ‘yan bindiga sun dorawa kauyuka a Zamfara nauyin biyan Naira miliyan 16 tare da sharadin wa’adi.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kakabawa kauyuka uku a karamar hukumar Bungudu ta Zamfara harajin miliyoyi.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun kakabawa kauyukan uku kudi har Naira miliyan shida ajihar da ke Arewa maso Yamma.

Rahoton Zagazola Makama ya bayyana cewa kauyukan da abin ya shafa sun hada da Gidan Saro, Maje da Fanda Haki da ke yankin Kekun Waje.

Wannan ba shi ne karon farko da mahara ke kakaba wa mazauna yankuna a Arewacin Najeriya haraji ba na makudan kudi.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments