Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiAtiku ya caccaki Wike kan barazanar harbe ɗan jarida

Atiku ya caccaki Wike kan barazanar harbe ɗan jarida

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da abin da ya kira “barazana mai haɗari da abin kunya” da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi wa ɗan jarida Seun Okinbaloye.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da abin da ya kira “barazana mai haɗari da abin kunya” da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi wa ɗan jarida Seun Okinbaloye.

A wata sanarwa da ofishinsa ya fitar, Atiku ya ce rashin hankali ne ga minista mai ci ya fito a talabijin kai tsaye yana cewa yana son harbin ɗan jarida saboda ra’ayinsa na aiki.

Ya ce: “Wannan ba kawai rashin hankali ba ne, alama ce mai firgitarwa ta yadda gwamnati ta nutse cikin rashin juriya, rashin bin doka da kuma cin zarafin iko.”

Ya kara da cewa wannan ba wasa ba ne, illa wata barazanagce kai tsaye mai muni, yana gargadin cewa idan masu iko suka fara amfani da harshen tashin hankali ga kafafen yada labarai, to dimokuradiyya na cikin barazana.

Atiku ya kuma zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kirkirar yanayi da ake takura wa masu suka, inda ya ce ana mayar da su masu laifi, yayin da tsoratarwa ke zama hanyar mulki.

Ya ce a kasashen da ke da cikakkiyar dimokuradiyya, irin wannan magana za ta sa a tilasta wa jami’in gwamnati yin murabus ko a kore shi, amma a Najeriya hakan na zama ruwan dare.

Ya tambaya: “Wane laifi ne ɗan jaridan ya aikata? Sai dai ya gargadi hadarin komawa jam’iyya daya kacal.”

Daga karshe, ya bukaci Nyesom Wike ya ba da hakuri ga Seun Okinbaloye da dukkan ‘yan jarida, tare da kira ga gwamnati da ta tabbatar da kare lafiyar ‘yan jarida a Najeriya.

Ya ce idan ba a dauki mataki ba, hakan zai tabbatar da tsoron da mutane ke yi cewa gwamnati na kara rungumar danniya da murkushe masu adawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments