Gwamnatin tarayya ta ƙarfafa aniyarta ta tabbatar da shirin “Renewed Hope” ta hanyar ƙaddamar da gagarumin shirin nan na bada tallafin kudi ga gidaje, watau HoPE-CT.
Ministan yaɗa labara, Mohammed Idris, wanda ya samu wakilcin Dr. Suleiman Haruna, ya bayyana wannan shiri a matsayin ɗaya daga cikin mafi tasiri wajen yaƙi da talauci a tarihin Najeriya.
A cewar Ministan, wannan shiri ya isa ga mazauna ƙasar sama da miliyan 9.2, kuma ana sa ran zai taɓa gidaje miliyan 15 a faɗin ƙasar nan nan ba da daɗewa ba, in ji rahoton Vanguard.
Ministan ya tabbatar da cewa gwamnati ta ware tallafi na musamman na N50,000 ga iyalai miliyan 3.6 waɗanda ke cikin mawuyacin hali domin rage masu raɗadin tattalin arziƙi.
Gwamnati ta jinjina wa ma’aikatar jinkai da rage radadin talauci bisa jajircewar da take nuna wa wajen gano ainihin mutanen da suka cancanci samun wannan tallafi a lungu da saƙo yau.