Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiLabaraiZa mu haɗa kai da ADC a wajen zaɓen Shugaban ƙasa —...

Za mu haɗa kai da ADC a wajen zaɓen Shugaban ƙasa — NNPP

Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa za ta haɗa kai da ADC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa za ta haɗa kai da ADC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Ladipo Johnson, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi, inda ya ce duk da ficewar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, NNPP za ta ci gaba da shiga zaɓe.

Ya ce NNPP za ta tsaya takara a wasu matakai, amma a matakin shugaban ƙasa za ta yi haɗin gwiwa da ADC, tare da yiwuwar haɗin kai a wasu muƙaman ƙasa.

Johnson ya bayyana cewa an yi tattaunawa da dama tsakanin shugabannin adawa kafin Kwankwaso ya yanke shawarar komawa ADC, inda ya ce hakan na da nufin haɗa kai domin ƙalubalantar jam’iyyar APC a 2027.A cewarsa, shugabannin adawa na ƙoƙarin haɗa ƙarfi a wuri guda domin samar da wata babbar haɗaka da za ta iya fafatawa da APC.

A ‘yan makonnin nan, Kwankwaso ya yi ganawa da manyan ‘yan siyasa ciki har da Rauf Aregbesola, Peter Obi, Seyi Makinde da Seriake Dickson domin ƙarfafa wannan haɗin kai.

Ana kallon wannan mataki a matsayin wani babban shiri na jam’iyyun adawa na ƙoƙarin kafa haɗakar siyasa mai ƙarfi kafin zaɓen 2027.

Sai dai wannan na zuwa ne a lokacin da rikici ke ƙaruwa tsakanin Kwankwaso da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya koma APC tare da wasu ‘yan siyasa, matakin da Kwankwaso ya soki yana mai cewa cin amana ne.

SourceChannels
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments