Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn yi zargin sakacin ma’aikatan jinya ya haddasa mutuwar yara biyu a...

An yi zargin sakacin ma’aikatan jinya ya haddasa mutuwar yara biyu a Kebbi

Rikicin zargi ya ɓarke kan ma’aikatan jinya bayan mutuwar yara biyu a Kebbi.

An kama wasu ma’aikatan jinya biyu bisa zargin hannu a mutuwar kananan yara mata biyu a asibitin gwamnati da ke Zuru, bayan rahotanni sun nuna yiwuwar kuskuren bada magani.

Rahotanni sun ce yaran, masu shekaru shida da uku, sun rasu ne a ranar 18 ga watan Maris bayan an yi zargin sakacin da ya shafi allurar da aka ba su yayin jinya a asibitin.

Jami’an tsaro sun tsare wadanda ake zargi a Birnin Kebbi, inda ake ci gaba da bincike domin gano hakikanin abin da ya haddasa mutuwar yaran.

Jaridar Daily Trust ta ambato gwamnatin jihar Kebbi, ta kafa kwamitin bincike mai mambobi tara karkashin jagorancin kwamishinan yada labarai da al’adu, Alhaji Yakubu Ahmed, domin zurfafa bincike kan lamarin.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments