Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya amince da biyan albashin watan Maris da wuri ga dukkan ma’aikatan gwamnati da masu karɓar fansho a fadin jihar, gabanin bikin sallah.
Matakin dai na da nufin sauƙaƙa wa ma’aikata da masu ritaya, tare da ba su damar yin shirye-shiryen bikin Sallah yadda ya kamata.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Muhammad Dantawasa, ya fitar ranar Litinin, gwamnatin ta ce an kammala duk shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da biyan albashi da fansho ga duk masu amfana a fadin jihar.