Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnan Zamfara ya ba da umarnin biyan ma’aikata albashin Maris da wuri...

Gwamnan Zamfara ya ba da umarnin biyan ma’aikata albashin Maris da wuri saboda Sallah

Ma’aikatan jihar za su karɓi albashin Maris da wuri bayan amincewar Gwamna Dauda Lawal.

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya amince da biyan albashin watan Maris da wuri ga dukkan ma’aikatan gwamnati da masu karɓar fansho a fadin jihar, gabanin bikin sallah.

Matakin dai na da nufin sauƙaƙa wa ma’aikata da masu ritaya, tare da ba su damar yin shirye-shiryen bikin Sallah yadda ya kamata.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Muhammad Dantawasa, ya fitar ranar Litinin, gwamnatin ta ce an kammala duk shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da biyan albashi da fansho ga duk masu amfana a fadin jihar.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments