Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHukumomi na nunawa Musulmai wariya – Majalisar Dinkin Duniya

Hukumomi na nunawa Musulmai wariya – Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa musulmai na fuskantar wariya a fadin duniya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya yi Allah wadai da abin da ya kira “nuna wariya” ga Musulmi a duk faɗin duniya.

Majalisar ta bayyana cewa musulmai da dama a sassan duniya, sau da yawa suna fuskantar nuna wariya daga hukumomi, da cire su daga harkokin tattalin arziki da zamantakewa, da tsauraran manufofin shige da fice, da kuma sanya musu idanu da bincike ba tare da wani dalili mai ƙarfi ba.

Sakatare Janar na Majalisar, Guterress ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙon da ya aika na bikin ranar yaƙi da ƙyamar Musulunci ta duniya a ranar 15 ga Maris.

Ya yi kira ga al’ummar duniya da su “sake jaddada aniyyar tabbatar da daidaito, haƙƙoƙin dan’adam, da martabar kowane mutum, ba tare da la’akari da addininsa ba.”

Guterres ya bayyana cewa waɗannan “munanan dabi’un suna samun gurbin zama ne sakamakon kalamai na nuna ƙiyayya ga Musulmai da kuma ƙiyayya kai-tsaye, wanda hakan ka iya haifar da cin zarafi da tashe-tashen hankula.”

SourceTRT
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments