Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiDakarun Hezbollah da sojojin Isra’ila sun fara gwabza yaƙi a Lebanon

Dakarun Hezbollah da sojojin Isra’ila sun fara gwabza yaƙi a Lebanon

An shiga gumurzu tsakanin Hezbollah da sojojin Isra’ila a yankin Lebanon.

Wasu faya-fayan bidiyo sun nuna yadda Sojin Isra’ila suka fara kwararuwa iyakar Lebanon ta kudanci don gwabza yaƙi da mayaƙan Hezbollah waɗanda suka sake faɗawa yaƙi da ƙasar ta Yahudu tun bayan da ƙasar da Amurka suka haɗa ƙarfi wajen ƙaddamar da yaƙi akan Iran.

Bayanai sun bayyana cewa tun a daren jiya aka faro gwabzawa tsakanin mayaƙan na Hezbollah da sojin Isra’ila a garin Khiam da ke iyakar ƙasar bayan da tun a kwanaki 2 da suka gabata ƙasar ta yahudu ta sanar da shirin ƙaƙƙarfar mamaya ta ƙasa a cikin Lebanon.

Isra’ila ta sanar da shirin ƙara faɗin mamayarta a cikin Lebanon, wanda ya sanya gwamnatin ƙasar janye ilahirin sojojinta da ke kan iyaka, a gefe guda ƙasar ta Yahudu ta yi gargaɗin cewa ba zata daina kai hare-hare ba har sai mahukuntan ƙasar sun ƙwace makamai daga hannun Hezbollah.

Garuruwan kan iyaka fiye da 200 Isra’ilar ta tilastawa tashi lamarin da ya raba mutane fiye da miliyan 2 da matsugunansu bisa alƙaluman hukumar kula da ƙaurar baƙi ta Majalisar ɗinkin duniya.

Zuwa yanzu mutane 850 Isra’ilar ta kashe a sassan Lebanon tun bayan tsananta hare-harenta kan rukunin gidajen jama’a a sassan Lebanon ciki har da hare-haren da ta kai da gubar Phosporus.

Gwamnatin Lebanon ta tabbatar da alƙaluman matattun yayinda ta ce akwai kuma wasu fiye da dubu 15 da suka jikkata.

Garin Khiam dai na daga cikin yankunan da mayaƙan na Hezbollah ke iko da su a kudancin Lebanon kuma galibi daga ciki suke kai hare-hare sassan Isra’ila.

Hezbollah na ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin sojin Isra’ila tare da iƙirarin cewa ta tafkawa ƙasar ɓarna mai yawa a wani yanayi da itama Isra’ilan ke iƙirarin kashe jagororin Hezbollah da dama.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments