Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMinistan tsaron Najeriya Christopher Musa ya gana da Shugabannin Rundunonin Soji

Ministan tsaron Najeriya Christopher Musa ya gana da Shugabannin Rundunonin Soji

Christopher Musa ya yi wata ganawa da Shugabannin rundunonin sojin Najeriya

Ministan Tsaro na Najeriya, Christopher Musa ya gayyaci dukkan Shugabannin Rundunonin Soji zuwa ofishinsa domin wani muhimmin taro kan hare-haren da aka kai kwanan nan a sansanonin soji daban-daban a yankin Arewa maso Gabas.

Waɗanda suka halarci taron a Hedikwatar Ma’aikatar Tsaro da ke Abuja a ranar Laraba sun haɗa da Shugaban Hafsoshin Tsaro, Olufemi Oluyede, da Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, Waidi Shaibu.

Sauran sun haɗa da Shugaban Rundunar Sojin Sama, Sunday Aneke; Shugaban Rundunar Sojin Ruwa, Idi Abass; da wakilai daga Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa da sauransu.

A baya bayan nan dai yan ta’adda sun kashe aƙalla jami’an soja uku masu mukamin Laftanal-Kanal a Jihar Borno, sannan sojoji da dama ma sun rasa rayukansu, yayin da daruruwan fararen-hula da aka sace har yanzu ke hannun masu garkuwa da su.

Da yake magana kafin a fara taron na sirri, Ministan Tsaron ya ce sun amince su sake duba dabarun yaƙi da ‘yanta’adda.

“Mun san cewa mun yi asarar wasu, amma asarar ta fi yawa a ɓangaren ‘yan ta’addan,” in ji Ministan Tsaron.

SourceDW
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments