Ministan wasannin Iran Ahmad Donyamali ya bayyana cewa ƴan wasan kwallon kafa na ƙasar ba za su je gasar cin kofin duniyar da za’ayi a ƙasar Amurka ba, sakamakon harin da ƙasar ta kai mata tare da Isra’ila.
Domyamali ya shaidawa gidan talabijin na ƙasar cewar sakamakon harin da ƙasashen suka kai Iran wanda ya hallaka shugaban su, babu dalilin da zai sa su halarci gasar.
Ministan ya ce a halin yanzu ƴaƴan su na cikin haɗari, saboda haka babu abinda zai sa su shiga gasar da za’ayi a watan Yuni wanda ƙasashen Amurka da Mexico da kuma Canada za su ɗauki nauyi daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli.
Domyamali ya ce sau biyu waɗannan ƙasashe ke kaddamar da yaƙi a kan Iran a tsakanin watanni takwas zuwa tara, wanda ya yi sanadiyar hallaka dubban mutane, saboda haka a kai gasar kasuwa, domin babu dalilin zuwa ƙasar.
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Saeid Iravani ya ce ya zuwa yanzu hare haren Amurka da Isra’ila ya hallaka fararen hula sama da 1,300.