Mai magana da yawun Khatam al-Anbiya, babban kwamiti na hadin gwiwar sojin Iran, ya yi barazanar cewa Iran za ta kai hari kan bankunan Isra’ila da na Amurka a yankin a matsayin ramuwar gayya ga abin da ya ce ‘an kai hari kan wani banki a Iran’.
Ebrahim Zolfaghari ya gargaɗi cewa “mutane a yankin kada su kusanci bankuna daga nisan kilomita ɗaya,” kamar yadda gidan talabijin na gwamnatin Iran, IRNA, ya ruwaito.
“Abokan gaba sun ba mu ‘yancin kai hari kan cibiyoyin tattalin arziki da bankuna” mallakar Amurka da Isra’ila, in ji Zolfaghari.
Haka kuma,an ruwaito cewa an kai hari kan wani gini na Bankin Sepah, bankin gwamnati dake Tehran.
A ranar Talata ne dai kafafen yada labaran Iran suka ruwaito cewa an samu wasu matsaloli a ayyukan Bankin Sepah da wani bankin gwamnati me suna Melli.