Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAmurka ta rufe ofishin jakadancinta da ke Najeriya saboda rikicin Iran

Amurka ta rufe ofishin jakadancinta da ke Najeriya saboda rikicin Iran

Rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ya tilasta wa jakadancin Amurka a Najeriya soke wasu ayyuka na wucin-gadi.

Ofishin Jakadancin Amurka da ke birnin Abuja ya sanar da rufe aikinsa na yau da kullum na wucin gadi, sakamakon yiwuwar barkewar zanga-zanga a babban birnin tarayyar, biyo bayan yaƙin Amurka da Iran

A wata sanarwa da Ofishin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce za a rufe ofishin har zuwa ranar Litinin, 9 ga Maris, 2026.

Sanarwar ta ce:

“Saboda yiwuwar zanga-zanga a Abuja, Ofishin Jakadancin Amurka zai kasance a rufe ga ayyukan yau da kullum har zuwa Litinin, 9 ga Maris, 2026.

“An dage dukkan alƙawuran neman biza da aka tsara yi a ranakun 4 da 5 ga Maris, tare da alƙawuran Sashen Kula da ‘Yan Ƙasar Amurka (ACS) na ranar 5 ga Maris, kuma an mayar da su zuwa mako mai zuwa.”

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan rahotanni sun nuna cewa an tsaurara matakan tsaro a sassa daban-daban na Abuja sakamakon yiwuwar zanga-zangar mambobin ƙungiyar (IMN) don nuna kin jinin kisan da Amurka da Isra’ila suka yiwa jagoran addinin Iran Ayatullah khamene’i.

SourceDNN
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments